An kafa dokar ta baci a tsibirin Lampedusa na Italiya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan gudun hijira daga kasar Tunisia

Magajin garin tsibirin Lampedusa na kasar Italia, ya kafa dokar ta baci, a sakamakon yawan bakin hauren da ba'a taba ganin irinsu ba da ke kwarara kasar Italia da ga Tunisia.

Yan kasar Tunisia kamar dubu biyar ne suka tsallaka zuwa tsibirin na Lampedusa ta cikin kwale-kwale.

An kuma katse hanzarin wani kwale-kwlen dauke da mutane talatin da ake ji Misirawa ne.

Ministan harkokin cikin gida na Italia, Roberto Maroni, ya yi gargadin cewar rikicin da ake samu a kasashen Tunisia da Masar, ya na iya haifar da kwararuwar bakin haure zuwa kasashen turai. Ya ce "wannan al'amari ne da zai iya haifar da wani yanayi cikin hanzari na samun sauyi a kasashen arewacin Africa, yadda kuma zai iya yin mummunan tasiri ga tsare tsaren zamantakewa na kasashen turai".

Tuni dai gwamnatin kasar Italia ta yi kira ga Kungiyar tarayyar turai da ta taimaka da kudade.