Yawaitar beraye: An kai muzuru fadar Fira Ministan Burtaniya

Larry Cat
Image caption Fira Minista Cameron ya yi maraba da Larry

Fira ministan Burtaniya ya yi maraba da muzurun da akai fadarsa da ke lamba 10 a Downing Street domin cinye berayen da ke fadar. Muzurun dan shekaru hudu, da ake kira Larry, a baya yana gidan kiwon karnuka da maguna na Battersea ne da ke London kafin akaishi fadar Fira Ministan.

Zuwan muzurun ya biyo bayan makonnin da aka shafe ana hasashen yadda za a shawo kan berayen da suka addabi fadar Fira Ministan dare-da-rana.

Larry ya isa fadar ne da misalin karfe 1:00 agogon GMT a ranar Talata, a wani keji da aka rufe.

Kamar yadda fadar ta bayyana, muzurun na da fasaha wajen "jiyo kanshi da kuma farautar beraye".

Babu tabbas ko za a baiwa muzurun damar shiga ko'ina a fadar Fira Minsitan, duk da cewa ana ganin muzurun ya iya zama da mutane.

Image caption Tuni dai Larry ya fara ayyukanta a fadar Fira Ministan

A wata sanarwa da aka fitar Mr Cameron ya ce: "Ina maraba da Larry zuwa sabon gidansa.

"Gidan kiwon karnuka da maguna na Battersea ne ya zakulo min shi.

"Ina fatan zai zamo wani kari mai mahimmanci a fadar Downing Street kuma zai yi maraba da masu ziyartar mu".

Kuma daga bisani mai magana da yawun Fira ministan ya ce Larry ya yi barci a yammacin Talata, "ba tare da nuna wata bakunta ba".

Ya ce Mr Cameron "ya gana da muzurun". Ya kara da cewa tunda muzurun na ofis ne ba gida ba, ma'aikatan fadar ne za su dinga biyan kudin abincinsa da kuma sauran abubuwansa.