Matsalar abinci a Niger

Image caption Wani yaro dake fuskantar yunwa a Nijar

A jamhuriyar Niger maganar samar da abinci ga 'yan kasar su Miliyan Goma sha biyar, da kuma dabbobin kasar wadanda zasu kai Miliyan arbain na kasancewa wani babban kalubale ga hukumomin kasar .

Bayan matsalar karancin abincin a shekarar data gabata, a yanzu haka an samu wasu manoman kasar da basu murmure ba daga matsalar, sakamakon ambaliyar ruwa a wasu sassan kasar ko kuma karamcin ruwa a wasu yankunan Niger din.

Sai dai wata hanya da hukumomin kasar Niger din da manoman kasar ke amfani da ita domin kaucewa matsalar yunwa, ita ce ta noman Rani ko aikin gandari.

Hakazalika hukumomin kasar sun ce tuni har suka fara daukar mataki domin ganin cewa an samu daidaito cikin bukatun jama'ar kasar.

Mai martaba sultan din Katsina Maradi Alhaji Ali Zaki Marimawa Katsinan Maradi ya shadaiwa BBC cewa suna sa ido wurin ganin cewa jama'a ba su yi almabaranci da abincin ba .