Yan Ivory Coast na ruguguwar janye kudi a bankuna

An ga dogayen layuka a bankuna a kasar Kot Divuwa, bisa tsoron da masu ajiyar kudi ke ji na rushewar bankuna a lokacin da ake ci gaba da kalubalantar juna a kan zaben shugaban kasar da aka yi a baya.

Bankin Starndard Chartered shi ne na hudu da a wannnan makon ya bayyana dakatar da ayyukansa a kasar.

An rufe galibin na'urorin dibar kudi da ke birnin Abidjan, ba a kuma iya karbar kudin duk wata takardar kudi ta ceki da aka rubuta.

Bankin BCEAO na yankin, a makon jiya ya gargadi bankunan kasuwanci cewa za su iya fuskantar takunkumi idan suka ci gaba da harka da gwamnatin Laurent Gbagba.