Wasu matasa sun yi wa ayarin Gwamna Lamido ruwan duwatsu a Hadejia

Wasu matasa cikin fushi a Hadejia sun yi wa Gwamna Sule Lamido na Jihar Jigawa ta Najeriya sowa tare kuma da jifar ayarinsa da duwatsu, yayin da ya halarci wani buki a garin.

Rahotanni sun ce, babbban jami'in dake kare lafiyar Alhaji Sule Lamidon ya sami rauni a jefe-jefen, kuma sai da 'yansanda suka shiga tsakani domin tarwatsa matasan masu bore.

Gwamna Lamido ya je garin ne domin halartar bukin sallar Maulidi da ake kira Salla Gani .

Rahotanni sunce tawagar Gwamnan ta fara gamuwa da gamon ta ne a unguwar Makwalla, a lokacin da wasu matasa suka yi yiwa tawagar kwanton bauna, suka kuma soma jifa da duwatsu da sauran ababuwan jifa.

Rahoton ya ce rikicin ya soma ne a karshen bukin sallar a lokacin da aka bukaci dan takarar Gwamna na Jama'iyar ANPP, kuma tsohon Mataimakin gwamna na Jihar, Barrister Ibrahim Hassan Hadejia yayi addu'ar rufe bukin.

Suka soma maganarsa ke da wuya sai taron jama'ar ya soma kururuwar "sai Barrister" da kuma "Sai mai sallah" tare da "Sai Gwamnan gobe".

Lokacin da Gwamna Sule Lamido ya tashi zai tafi sai taron jama'ar ya dauki kururuwar, "ba ma yi".

Nan da nan dai yansanda suka shiga suka tarwatsa matasan da suka fusata don Gwamnan ya samu ficewa daga wurin.

Kwamishinan Yansanda na Jihar ta Jigawa dai ya ce shi ba shi da labarin afkuwar lamarin saboda ba a gayyace shi wurin bukin ba.

Haka nan shi ma darektan hulda da manema labarai na gwamnan Malam Umar Kyari, ya musanta faruwar al'amarin.

Wannan lamari dai ya faru ne yayinda babban zaben kasar na watan Afrilu ke dada karatowa.