Mutane arba'in sun jikkata a boren kasar Libya

Shugaba Muammar Gaddafi
Image caption Shugaba Muammar Gaddafi na Libya

An samu karin bayani game da rikici na farko a Libya tun bayan tunzurin da aka samu a Masar da Tunisia makwabatan kasar.

Masu zanga-zanga a birnin Benghazi sun yi ta rera taken nuna kyamar gwamnatin Libyar.

Sun yi taho mu gama da 'yansanda da kuma mutane masu goyon bayan gwamnatin, tare da jifa da duwatsu da bama - baman fetur a kan motoci.

'yan sanda kuma sun maida martani da harsasan roba.

Mutane kusan arba'in ne suka samu raunuka a zanga zangar, haka nan kuma an ce kimanin mutane dubu biyu ne dai suka gudanar da zanga zangar a cewar wadanda suka ganewa idanunnasu.