Tottenham ta yi galaba akan AC Milan

Image caption Peter Crouch na murnanr zura kwallo.

Tottenham ta samu nasara a bugun farko da ta yi tattaki zuwa Italiya, inda ta doke AC Milan da ci daya mai ban haushi a gasar zakarun Turai.

Peter Crouch ne ya zura kwallon ana minti 80 da wasan bayan Aaron Lennon ya kawo kora, inda ya rika zilleya 'yan wasan bayan AC Milan sannan ya sanyawa Crouch kwallon.

Mai tsaron gidan Tottenham Heurelho Gomes ya taimakawa kungiyar har sau biyu, inda ya tare kwallayen Mario Yepes .

Zlatan Ibrahimovic ya zura kwallo dab da kafin a tashi wasan amma alkalin wasa ya hana, inda ya zarge shi da tade dan wasan Spurs.

An dai kammala wasan cikin wani hali, inda dan wasan Milan Genaro Gattuso ya fusata sannan ya yi mataimakin kocin Tottenham Joe Jordan karo.