Guguwar neman sauyi a Bharain

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An jikkata masu zanga-zanga da dama.

Karuwar zanga zangar da ake samu a kasar Bahrain dake yankin Gulf ya janyo an fara nuna damuwa cewa, mai yuwa ita ma wannan guguwa ta yi awon gaba da tsarin siyasarta, kamar yadda ta faru a kasashen Tunisia da Masar. Hukumomi a Bahrain sun fi daukar tsauraran matakai a kan masu zanga zangar a inda aka kashe wasu daga cikinsu. Guguwar bore a yankin Gabas ta Tsakiya ta yadu daga kasar Tunisia a arewacin Afirka ta ratsa ta kasar Larabawa mafi muhimmanci a duniya, wato Masar, yanzu kuma tana kewayawa a yankin Gulf.

Sanadin boren dai iri daya ne a fadin yankin, to amma na Bahrain kyakkyawan misali ne na yadda al'amuran cikin gida kan yi tasiri a kan siyasar ko wacce kasa.

'Ba matalauciyar kasa ba ce'

Kasancewar tana da arzikin man fetur, Bahrain ba matalauciyar kasa ba ce.

Don haka boren da ake yi a can ya ginu ne a kan zaman doya da manjan da aka dade ana yi tsakanin 'yan Shi'a mafiya rinjaye da kuma masu mulkin kasar 'yan Sunni.

'Yan sauye-sauyen siyasar da masu mulkin suka aiwatar dai bai gamsar da bukatun al'ummar ba.

Abu ne mai wuya a iya tantance hakikanin bambance-bambancen da ke tsakanin al'ummar kasar, musamman saboda manufofin gwamnati na ba da shaidar zama dan kasa ga 'yan Sunni daga wasu kasashen, al'amarin da ke kara bakanta ran 'yan Shi'a masu rinjaye.

Tarwatsa zanga-zanga

Hukumomin a kasar ta Bahrain dai sun jajirce don ganin sun tarwatsa zanga-zangar da akasari ta lumana ce ta hanayar amfani da karfi; hakan kuma wani karin bambanci ne tsakanin boren Masar da na Bahrain.

Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Masu zanga zanga a Bharain

Da yawa daga cikin wanda ake dauka don yin aiki a rundunonin tsaron kasar dai, kamar a sauran kasashen yankin Gulf, mutanen wasu kasashen Musulmi ne irinsu Pakistan da Yemen; don haka zai yi wuya su marawa al'ummar kasar baya.

Kasar ta Bahrain dai tana da muhimmanci a yankin, kasancewarta hedkwatar runduna ta Biyar ta sojojin ruwan Amurka.

Wata hanyar da ta ratsa ta cikin teku ta hada kasar ta Bahrain da yankin da 'yan Shi'a suke a Saudi Arebiya; don haka mahukunta a Riyadh sun zuba ido sosai a kan abubuwan d ake gudana a Bahrain.

Mahukuntan Iran ma, wadanda tun taletale suke da wani muhimmin muradi a tsibirin na Bahrain suna zuba ido sosai.