An ci gaba da zanga zanga a birnin Benghazi

Libya Hakkin mallakar hoto AFP

An bayar da rahoton yin wata kasaitacciyar zanga zanga a birni na biyu mafi girma a kasar Libya, bayan kiran da aka yi na gudanar da zanga zangar ranar fushi.

Kamar dai yadda shedu suka ce dubban mutane ne suka fita kan titinan birnin na Bengazi suna kururuwar "Jama'a na son hambarar da Kanar Gaddafi"

Kanar Gaddafi dai ya shafe fiye da shekaru 40 ya na mulkin a kasar ta Libya.

Shafunan internet na 'yan hamayya sunce an kashe mutane da yawa a can, to amma babu wata majiya da zata iya tabbatar da hakan.

Haka nan kuma akwai rahotannin da ke cewar an yi zanga zanga a Zenten da kuma Al Baida. Wata jaridar kasar ta Libya ta ce an sallami shugaban hukumar tsaro na birnin sakamakon mutuwar mutane 2 a zanga