Dokar yaki da ta'addanci a Najeriya

Malaissar dokokin Nigeria

Majalisar datawan Najeriya ta amince da kudurin doka kan yaki da ta'addanci a Najeriya.

Shi dai wannan kudurin doka ya tanadi hukunci akan aikin ta'addanci da kuma samar da kudaden da ake amfani dasu wajen aikata ta'addanci.

Kudurin dokar ya kuma tanadi hukunci akan tunzura mutane domin su aikata ta'addanci.

Majlisar ta ce Kudurin zai kuma kaiga kafuwar wata hukuma ta musaman wadda za'a dorawa alhakin yaki da ta'adanci a kasar.

Tashe-tashen bama-bamai daga karshen bara na daga cikin dalilan da suka karfafa kokarin ganin an samar da wannan doka.

A baya dai shugaba Goodluck Jonathan ya rubutawa 'yan majalisar dokokin Nigeriar wasiku ya na kiran da su hanzarta kammala aiki akan wannan doka.