Mutane goma sun halaka a Tanzania

Image caption Shugaba Kikwete na Tanzania

Jami'an wani asibiti a birnin Darus-salam na kasar Tanzania, sun ce akalla mutane goma ne suka halaka,yayinda sama da sittin sun sami raunuka, sakamakon fashewar wasu abubuwa a wurin ajjiye makamai dake kusa da filin saukar jiragen sama.

Wani mai magana da yawun rundunar sojin kasar yace fashe fashen abubuwan sun auku ne da tsakar daren jiya bisa hatsari .

Ya ce an rufe babban titin dake zuwa cibiyar ajjiye makaman.

Wakilin BBC ya ce jami'an rundunar sojin kasar, sun umarci mutanen dake zaune kusa da inda abin ya auku, da su tattara inasu inasu su bar wajen, sannan kuma an dakatar da saukar jirage a filin saukar jiragen sama na birnin.

Wannan shine karo na biyu da za'a samu lamarin da ya shafi makaman soji a Tanzania.

Na farkon dai, ya auku ne a watan Aprilu na shekerar 2009 abun da kuma ya yi sandiyar mutuwar mutane ashirin yayinda sama da dari uku su ka sami raunuka.