Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Barin ciki

Hukumar dake kula da tsarin kiwon lafiya a Birtaniya, NHS ta ce akalla, kashi 20 cikin dari na cikin da aka samu kan kare ne a bari, inda hukumar ta nuna cewa akwai yiwuwar alkaluman sunfi haka don saboda matan da kan samu bari ba sa son yin magana akai.

Haka kuma a cewar NHS, bari wani abu ne da ga wasu matan su kan yi bari ne kamar sau daya ko kuma jefi-jefi sai kuma su ci gaba da haihuwa lafiya. Amma ga wasu matan su kan yi ta jera barin ne.

Kuma matan da ke wannan rukunin su ne wadanda ke samun bari kamar sau uku a jere zuwa sama da hakan. Sai dai kashi 75 cikin dari na matan da kan jera barin daga baya kuma su kan zo su cigaba da haihuwa lafiya.

Bari abune da ke faru yau da kullum, fiye da yadda mutane ke zato. Daya cikin kowane ciki biyar da mata ke samu na karewa ne a bari wato kimanin kashi 20 cikin dari na matan da suka samu juna biyu akanyi barinsu.

Ga wasu matan bari yakan zo ya wuce ba tare da ya dame su ba, amma ga wasu kuwa ya kan janyo musu damuwa matuka. shirin mu kenan na wannan makon ayi sauraro lafiya.