Ivory Coast za ta kwace bankunan kasashen waje

Ivory Coast Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Masu ajiya suna ta ruguguwar zuwa bankuna domin cire kudadensu

Laurent Gbagbo, wanda ya ki amincewa ya sha kaye a zaben shugaban kasar Ivory Coast, ya ce zai mayar da bankuna kasashen waje da dama mallakar gwamnati.

Shugaba ya yi barazanar daukar matakin ne bayan da bankunan suka dakatar da ayyukansu a kasar, bisa rikicin siyasar da ake fama da shi.

Mr Gbagbo ya ki sauka ne daga mulki, bayan da ya sha kaye a hannun Alassane Ouattara, a zaben da aka yi a watan Nuwamba. Tsarin bankuna na kasar ta Cot D'voir wadda ta fi kowacce arzikin Cocoa a duniya na gab da wargajewa, kamar yadda masu nazari akan al'amurra ke bayyanawa, saboda yadda masu ajiya a bankuna suke ta ruguguwar zuwa bankuna domin cire kudadensu.

Masu sukar lamirin Shugaba Gbagbo, na fatan cewar rufe bankunan da kuma takunkumin hana sayen Cocoa'n da kasashen duniya suka sanyawa kasar, za su taimakawa wajen ganin bai samu uzurin biyan albashin sojojin da sauran ma'aikatan gwamnatin da ke mara masa baya ba.

Amma wani masani akan harkokin bankuna, ya shaidawa BBC, cewar mayar da bankunan karkashin ikon gwamnati da kuma janye kasar daga cikin kungiyar kasashe masu amfani da kudin Sefa.

Kuma hakan na nufin Mr Gbagbo, na iya buga duk irin yawan kudin da ya ke son bugawa, domin tabbatar da gwamnatinsa na ci gaba da aiki.

To amma ya yi gargadin cewar akwai babban hadari wanda zai iya kai ga kasar fuskantar irin hauhawar farashin kayan da suka durkusar da tattalin arzikin kasar Zimbabwe.