Ana cigaba da zanga zanga a Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Gadafi

Ana cigaba da gudanar da zanga zanga a gabashin birnin Benghazi na kasar Libya.

Lamarin dai ya shafi birane hudu dake kasar, ko da yake komai na tafiya dai dai a Tripoli babban birinin kasar.

Wani bidiyo da aka saka a shafin intenet na you tube ya nuna yadda mutane suka kewaya mottoci da aka cinama wuta da kuma gine gine da suka kamu da wuta.

Wadanda suka shaida lamarin da idanunsu sun ce an gudanar da karamar zanga zanga a birnin Benghazi da safiyar jiya amma yawan masu zanga zangar ya karu matuka da tsakar dare jiya.

Sun ce dubun dubatar mutane sun hau kan titunan da ke sassa daban daban na birnin.

Sun kuma ce an yi ta harbe harben bindigogi.

Wani likata a asibitin Jalla dake birnin ya ce an kawo gawarwakin mutane goma a daren jiya .

Libya dai ita ce kasa ta hudu a Arewacin Afrika da jama'a zasu yi bore.