Masu zabe sun fara kada kuri'a a Uganda

Hakkin mallakar hoto Majimbo Kenya
Image caption Dr Kiza Besigwe

Jama'a sun fara kada kuri'a a zaben shugaban kasa da kuma majalisar dokoki na Uganda.

Ana dai sa ran cewa shugaba Yoweri museveni ne zai lashe zaben sai dai ana ganin watakila wanan zaben ya kasance wani abun da zai janyo wata takaddama.

A zabukan da gudanar a shekaru biyar da suka gabata an rika matsawa da kuma tsorata yan adawa amma a wanan karon abokin hammaya shugaban kasar Dr Kiza Besigwe da kuma sauran yan takarar shugaban kasar sun samu damar gudanar da yakin neman su cikin kwanciyar hankali.

Dakta Besigye dai ya sha kaye daga hanun Mr Museveni a zabukan kasar guda biyu da aka gudanar ,wadanda suka janyo cece kuce.

Ya kuma ce idan har ya sake faduwa a wanan zabe zai yi kira ga jama'ar kasar su gudanar da zanga zanga.

Shi kuwa shugaba Museveni ya lashi takobin ganin cewa ya kule duk wani wanda ya yi kokarin tada zaune tsaye a Uganda.

Ya ce abubuwan da suka faru a Arewacin nahiyar Afrika ba za'a taba amincewa da su a kasar Uganda ba.