Zanga-zangar adawa da gwamnati a Bahrain

Zanga zanga a Bahrain Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Zanga zanga a Bahrain

A Bahrain, masu zanga-zanga sun sake kwarara zuwa dandalin Pearl Square, a Manama babban birnin kasar, domin cigaba da nuna adawa da gwamnati.

Da farko an yi taho-mu-gama tsakanin 'yan sandan kwantar da tarzoma da kuma masu zanga-zangar.

Jami'an 'yan sandan sun bude wuta da barkonon tsohuwa, da kuma yin amfani da kananan bindigogi, amma daga baya suka ja da baya, inda suka kyale daruruwan masu zanga-zangar suka koma dandalin na Pearl Square.

Shugabannin Bahrain din sun nemi sojoji da su janye daga birnin Manama.

Masu zanga-zangar, wadanda suke neman gwamnatin kasar ta sauka, sun yi watsi da wannan yunkuri da cewa yayi kadan.