Amurka ta bijirewa Kwamitin Sulhu

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Susan Rice
Image caption Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Susan Rice

Amurka ta yi watsi da wani kudirin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya yi tir da ginin matsugunan da Isra'ila ke yi a yankunan Falasdinawan da ta mamaye.

Kudirin, wanda ya ambaci gine-ginen da Isra'ila ke yi da cewa haramtattu ne kuma kafar ungulu ne ga shirin samar da zaman lafiya, ya samu gagarumin goyon baya.

Kasashe da dama ne dai suka gabatar da kudirin a gaban Kwamitin Sulhun, sauran mambobin kwamitin kuma suka amince da shi.

Saboda haka ne Amurka ta zama saniyar ware lokacin da ta ki amincewa da kudirin.

Jakadiyar Amurka Susan Rice ta yi kakkausar suka a kan gina matsugunan na Isra'ila, to amma a cewarta, gabatar da kudirin a gaban Majalisar Dinkin Duniya zai jefa shirin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya cikin rudani.

Gwamnatin Obama dai ta yi kokarin kaucewa daukar wannan mataki; to amma ta mika wuya ga matsin lambar Isra'ila da 'yan barandanta a Majalisar Dokokin Amurkan bayan ta kasa shawo kan Falsadinawa su janye kudirin su musanya shi da wani mai tattausan lafazi.

Sai dai matakin da Amurkar ta dauka ka iya kara zubar da kimar ta a kasashen Larabawa.