An tarwatsa magoya bayan Alassane Ouattara

Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Alassane Ouattara

Jami'an tsaro a kasar Cote d Ivoire sun harba barkonon tsohuwa kan magoya bayan Alassane Ouattara, wanda kasashen duniya suka ce shine ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi.

Daruruwan masu zanga-zanga sun taru a babban birnin kasuwancin kasar, Abidjan, domin yin kira ga shugaban dake kan mulki, Laurent Gbagbo, na ya mika mulki.

Mr Gbagbo ya kafa dokar hana yawon dare ta kwanaki uku a kasar tun daga jiya, bayan da magoya bayan Mr Ouattara suka yi kiran da a sami juyin-juya hali a kasar, kamar yadda ta faru a Masar.