Makiyayan Nijar sun koka da rashin tsaro

Salou Djibo
Image caption Shugaban Mulkin Soja na Nijar Salou Djibo

A jamhuriyar Nijar, gamayyar makiyaya Fulani da Abzinawa na Jihar Tillabery da ke iyakar kasar da Mali ta koka ga Majalisar Tuntubar Juna ta kasar bisa hare-haren da ta ce wadansu masu dauke da makamai na kai musu.

Gamayyar ta ce masu hare-haren sun kai ga hallaka wasu makiyayan tare da yin awon gaba da dukiyoyinsu, ciki har da shanu da rakuma.

Shugaban kungiyar makiyayan, Malam Diallo Abubakar, ya ce har mutane ma maharan su kan dauke.

“Kwanan nan wadansu sojojin Mali sun shigo kasarmu suka kama mutum uku suka [tafi da su]; sai da [mutanen uku] suka biya jaka dari takwas da hamsin na CFA sannan aka sako su”.

A shekarun baya dai an sha shirya tarurruka tsakanin hukumomin kasar ta Nijar da takwarorinsu na Mali domin shawo kan wannan matsalar amma hakan bai yi wani tasiri ba.

Daya daga cikin matakan da kasashen biyu suka dauka shi ne sintirin hadin gwiwa tsakanin sojojin Nijar da na Mali a kan iyakoki tare da baiwa sojojin kasashen biyu damar shiga cikin kowacce daga kasashen domin farautar masu laifi.