Bahrain:Masu zanga-zanga sun yi kane-kane a dandalin Pearl

Hakkin mallakar hoto AP

A Bahrain dubban masu zanga zanga sun yi kane-kane a dandalin Pearl Square, wanda ke tsakiyar Manama, babban birnin kasar.

Jiya Asabar, Yarima mai jiran gado, Sheikh Salman bin Hamad Al-Khalifa, ya umurci sojoji da tankunan yaki masu sulke da su janye.

Sarkin Bahrain din, Hamad bin Isa Al-Khalifa, shi ne ya ba 'dan nasa aikin bude tattaunawa tare da 'yan adawa.

Sai dai a cewar shugabannin 'yan adawar, ba za su shiga tattaunawar ba har sai an cika wasu sharudda.

Mutanen da ke zanga zangar su na son ne a koma mulkin dimukuradiyya a cikin ruwan sanyi.