An saki wani dan adawar daga kaso a Cuba

Ivan Hernandez Hakkin mallakar hoto a
Image caption Dan adawar kasar Cuba, Ivan Hernandez

Gwamnatin Cuba ta saki wani dan adawa wanda ya ki amincewa da sharadin ya tafi gudun hijira.

Yanzu haka dai dan adawar, Ivan Hernandez, wanda dan jarida ne mai zaman kansa, ya koma gidansa da ke garin Colon mai tazarar kilomita dari biyu daga Havana.

A wata hira ta waya, Mista Hernandez ya ce zai ci gaba da fafutukar da ya ke yi ta neman 'yancin fadin albarkacin baki; kuma zai komawa aikin jaridar da ya ke yi kafin a yanke masa hukunci.

An dai yankewa Mista Hernandez hukuncin zaman kaso na shekaru ashirin da biyar ne bayan wani kame na 'yan adawa a shekarar 2003.

Kasar ta Cuba dai ta na daukar 'yan adawa a matsayin karnukan farautar Amurka.

A wani matakin shiga-tsakani na Cocin Roman Katolika a bara ne dai Shugaban kasar, Raul Castro, ya amince ya saki 'yan adawa hamsin da biyu da ke tsare.