Jama'a na zanga zanga a Morocco

Dubban masu zanga zanga a Morocco Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban masu zanga zanga a Morocco

A Morocco, dubban masu zanga zanga sun hallara a Rabat, babban birnin kasar, domin neman Sarki Mohammed ya rage yawan ikon da yake da shi.

Rahotanni sun ce, 'yan sanda sanye da kayan sarki sun nisanta kansu daga wurin gangamin.

Wata kungiya ce mai kiran kanta: Kungiya mai neman kawo sauyi ta ranar ashirin ga watan Fabrairu, ta kirkiro zanga zangar.

A yanzu haka an ce kungiyar tana da mabiya dubu 19 a shafinta na Facebook.

Sai dai a cewar masu lura da lamurra, da wuya zanga zangar ta sami goyon bayan jama'a, saboda da ma Sarki Mohammed mutum ne mai ra'ayin sauyi, kuma tattalin arzikin kasar ta Morocco yana bunkasa.