CDS ta bayyana goyon baya ga MNSD a Nijar

Rumfar zabe a Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rumfar zabe a Nijar

A jamhuriyar Nijar, yayinda ya rage makwanni uku kacal a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, wadansu jam'iyyun siyasa sun bayyana goyon baya ga dan takarar jam'iyyar MNSD Nassara, Elhaji Seini Oumarou.

Jiya ne dai jam'iyyar CDS Rahama ta tsohon shugaban kasa, Elhaji Mahamane Ousmane, da kuma kawancen mata magoya bayan tsofaffin jam'iyyu masu mulki a karkashin inuwar AFDR, suka bayyana goyon bayansu ga dan takarar na jam'iyyar MNSD Nassara.

Wani kusa a kwamitin zartarwa na jam’iyyar ta CDS Rahama, Elhaji Doudou Rahama, ya ce sun dauki wannan mataki ne don su cika alkawari.

“Magoya baya duka na CDS Rahama na kasa gaba daya kuma da na kasashen waje sun ce dan takarar da za a goyawa baya [shi ne] Elhaji Seini Oumarou.

“Wannan magana [ta nuna cewa] magoya bayan Rahama sun yi diyauci sun rike alkawari, sun rike amana; da ma abin da aka san mu da shi ke nan—muka yi shekara tara da rabi, muka zauna a bayan [tsohon Shugaban kasa] Tandja”.

Kwanakin baya ne dai wadansu ’ya’yan jam’iyyar ta CDS RAHAMA suka bayyana goyon bayansu ga dan takarar PNDS Tarayya, Elhaji Mahamadou Issoufou.

Karin bayani