An kai harin bomb kan ofishin dan takarar Gwamna

Masu fafutuka a yankin Niger Delta

An kai hari a kan ofishin yakin neman zabe na dan takarar mukamin gwamna a Jihar Bayelsa, Karkashin Jam'iyar Labour, Chief Timi Alaibe , a garin Ogbia.

An kai wannan hari ne a ayayin da dan takarar ke kokarin shirin kaddamar da yakin neman zaben sa a ta garin na Ogbia , da ke cikin Jihar Bayelsa a yankin kudu maso kudancin Nigeria mai arzikin Man Petur.

Kakakin Huykumar Yan-sanda a Jihar ta Bayelsa, ASP Eguavon Emokpai, ya tabbatar wa BBC, faruwar al'amarin.

Ya kuma ce ba a yi asarar rai ba, amma dukiya ta salwanta.

Dama dai a can baya an taba kaiwa ayarin dan takarar Jam'iyyar ta Labour hari a Jihar ta Bayelsa.