Shugabannin Afirka biyar za su Ivory Coast

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast

Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, da wasu shugabannin kasashen Afirka hudu, za su ziyarci Ivory Coast don tattaunawa a kan hanyoyin kawo karhsen rikicin siyasar kasar.

Wannan ne dai yunkuri na baya-bayan nan—wanda kuma wasu ke ganin shi ne na karshe—na warware rikicikin siyasar Ivory Coast wanda ya ke gab da durkusar da tattalin arzikin kasar.

Shugabannin—na Afirka ta Kudu, da Burkina Faso, da Tanzania, da Cadi, da Mauritania—sun gana jiya Lahadi a babban birnin kasar Mauritania, Nouakchott, don jin rahoton kwamitin kwararrun da kungiyar Tarayyar Afirka ta kafa wanda ya shafe mako guda a Ivory Coast yana tattaunawa da bangarorin da ke rikici da juna.

Shugabannin dai za su ziyarci kasar ne a daidai lokacin da ta ke shure-shure.

A cikin mako gudan da ya gabata ne dai manyan bankunan kasuwanci na kasar suka rurrufe kofofinsu, sannan harkar kasuwanci ta tsaya cak.

A yanzu dai jiragen ruwa kalilan ne ke lekawa tashoshin jiragen ruwan kasar guda biyu, bayan Tarayyar Turai ta sanya musu takunkumi.

Mista Gbagbo dai ya yi yunkurin hana zanga-zanga ta hanyar sanya dokar hana fitar dare a fadin kasar, yayinda firayim minista a gwamnatin Mista Ouattara, Guillaume Soro, ya yi kira ga al'ummar kasar su fito su yi juyin-juya-hali irin na Tunisia da Masar.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce tun bayan fitar da sakamakon zaben shugaban kasar a farkon watan Disambar bara, kusan mutane dari biyar, akasarinsu magoya bayan Mista Ouattara, sun rasa rayukansu.