Zanga-zanga ta watsu zuwa birnin Tarabulus

Masu zanga-zanga a Libya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zanga a Libya

A karo na farko, zanga-zangar da ake yi ta kin jinin gwamnati a Libya ta watsu zuwa tsakiyar babban birnin kasar, Tarabulus, wato Tripoli.

Rahotanni sun bayyana cewa dimbin masu zanga-zanga sun kwashe sa’o’i da dama a titunan birnin a daren jiya Lahadi suna kiran a kawar da gwamnatin Kanar Muammar Gaddafi.

An kuma ba da rahoton jin karar bindigogi da kona gine-ginen ciki har da ofisoshin 'yansanda.

An dai bayar da rahoton cewa da asuba birnin ya yi tsit, ko da ya ke ana iya jin karar harbin bindiga jefi-jefi.

Wannan ya biyo bayan karbe iko da birnin Benghazi ne da rahotanni suka ce masu zanga-zangar sun yi.

Daya daga cikin 'ya'yan Kanar Gaddafi, Saif al-Islam al-Gaddafi, ya yi jawabi a gidan talabijin na kasar yana alkawarin shiga tattaunawa nan da sa'o'i arba'in da takwas, da nufin gyaran kundin tsarin mulki, wanda ya ce zai haifar da sauye-sauyen siyasa.

Ya kuma kara da cewa zaman lafiya da hadin kan kasar Libya na fuskantar barazana daga 'yan-aware, sannan ya ce matasa a shirye su ke su bayar da jininsu don kare kasar.

“Daukacin matasan Libya a shirye suke su sadaukar da rayukansu.

“Kuma ina tabbatar muku, ya ku 'yan uwana 'yan Libya, muna tare da ku a wannan gwagwarmaya ba za mu ba ku kunya ba”.

Karin bayani