Jakadun Libya sun yi kiran akai dauki Libya

Masu zanga zanga a Libya Hakkin mallakar hoto Reuters

Jami'an diflomasiyyar kasar Libya a Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga kasashen duniya da su sa baki game da abin dake faruwa a kasarsu.

Mataimakin jakadan Libya a Majalisar, Ibrahim Omar Al Dabashi, ya yi kiran da a baiwa 'yan kasarsa kariya daga abinda ya kira, kisan kare dangin da hukumomin Libya ke yi a kasar.

Ya ce kamata ya yi a kafa dokar hana sauka da tashin jirage a Tripoli babban birnin kasar, inda wasu rahotannin da ba a tabbatar ba suka nuna cewa wani jirgin yaki ya yi harbi kan masu zanga zangar adawa da gwamnati.

Wasu rahotanni da ba'a tabbatar da su ba na cewa Shugaba Gaddafi ya bar kasar ta Libya.