An fara kwaso 'yan Najeriya daga Libya

Gwamnatin Najeriya ta fara kwaso al'ummarta da ke kasar Libya, yayinda ake ci gaba da fuskantar rashin tabbas a kasar.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ce wato NEMA, ke gudanar da aikin.

A daren Asabar wayewar Lahadi ne rukunin farko na 'yan Najeriya suka sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja.

Wannan dai ya biyo bayan tashe tashen hankulan dake faruwa a Libya, inda masu zanga zangar nuna adawa da gwamnatin Kanar Mu'ammar Gaddafi ke kokarin ganin sai ya yi murabus daga mulkin kimanin shekaru arba'in da ya ke yiwa kasar.

Dakarun da ke biyayya ga Kanar Gaddafi sun mayar da zazzafan martani da ya salwantar da rayuka da dama tare da jikkata wasu.

Lamarin kuma da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashen duniya suka yi Allah Wadai da shi.