Kalubalen da ke gaban gwamnati ta Gaba

Nigeria
Image caption Da dama na ganin wannan zaben shi ne damar komawar Najeriya kan tafarkin ci gaba

Duk da cewa shugaba Goodluck na ganin ya taka rawar gani a shekara dayan da ta wuce, tun bayan da ya hau karagar mulki bayan rasuwar marigayi Umaru Musa 'Yar Adua, 'yan Najeriya da dama na ganin akwai muhimman kalubale a kasar, wadanda suka hadar da:

Naija Delta: Duk da cewa gwamnatin marigayi Umaru Musa Yar'adua wadda Goodluck Jonathan ya gada ta yiwa 'yan gwagwarmayar yankin Naija Delta tayin afuwa, sai dai rashin aiwatar da shirin kamar yadda ya kamata ya sa 'yan gwagwarmayar yankin Naija Deltan komawa gidan jiya inda suka koma sace mutane da kai hare-hare kan kamfanonin mai.

Don haka wata babbar matsala ce da shugaba na gaba zai gada.

Batun shawo kan matsalar yawan sace-sacen mutane da kasha-kashe, wani babban kalubale ne ga sabuwar gwamnatin da za'a zaba.

Matsalar tsaro: Rashin tsaro, fashi da makami da ranar Allah, kashe-kashen siyasa, da dai sauransu, batutuwa ne da ke ci gaba da dabaibaye Najeriya.

Akwai rikicin 'yan Boko Haram a jihar Borno; ga rikicin kabilanci da addini a Jos- jihar Filato da kuma na masu fafutuka a yankin Naija Delta.

Wata matsala da kasar ke fuskanta ita ce ta tashe-tashen bam da ake ta samu tun bayan wanda aka kai a Abuja ranar bikin 'yancin kan Najeriya.

Yaki da cin-hanci: Yaki da cin hanci da rashawa da hukumar EFCC ke yi ya ragu tun bayan tafiyar tsohon shugaban hukumar Nuhu Ribadu, wanda aka cire shi daga mukamin cikin wani yanayi da aka yi ta takaddama akai.

Tabbatacciyar Wutar Lantarki: Kama daga Obasanjo zuwa Yar'adua yanzu kuma Jonathan, kowannensu ya yi alkawarin samar da wutar lantarki a duk fadin kasar.

An narka biliyoyin nairori a wannan bangare, amma ba wani sakamako da za'a ce an samu. Dubban masana'antu sun rufe sabili da rashin wutar lantarki a duk fadin kasar.

Tattalin Arziki: Har yanzu talauci na nan bai kauba a Najeriya duk kuwa da dinbim biliyoyin dalolin da kasar ke samu ta man fetur din da take siyarwa, tun bayan da kasar ta koma mulkin farar hula a shekarar 1999.