An sako ma'aikatan AREVA uku daga cikin wanda aka sace

A jamhuriyar Nijar, gwamnatin kasar ta tabbatar da cewa 'yan kungiyar Al Qa'ida reshen Maghreb sun sako uku daga cikin ma'aikatan kamfanin AREVA mai hako ma'adinai a yankin arewacin kasar.

Sai dai sauran ma'aikatan turawa su hudu na ci gaba da kasancewa a hannun 'yan kungiyar ta Al Qa'ida.

A watannin da suka gabata ne dai aka sace ma'aikatan kamfanin na AREVA su bakwai.

Gwamnatin Nijar dai ta nuna rashin jin dadinta game da faruwar wannan al'amari, amma duk da haka ta yi maraba da sakin uku daga cikin mutanen bakwai.