An sabunta: 3 ga Maris, 2011 - An wallafa a 18:18 GMT

Kuri'arka 'Yancinka

Zaben Najeriya 2011

Wannan ne karo na hudu da ake zabe tun bayan komawar kasar tafarkin dimokradiyya

A tsari irin na Demokradiyya, jama'ar kasa ba su da wani makami da zai taimaka musu wajen shiga a dama da su a harkokin mulkin kasa da ya wuce kuri'arsu wacce za ta basu damar zabar wadanda za su shugabance su.

Irin wannan tsari har ila yau, zai baiwa jama'a damar kawar da duk wanda suka ga bai dace ya shugabance su ba.

Akasin tsarin mulki irin na soji, tsarin demokradiyya yakan baiwa jama'a damar zaba su more, su kuma tantance a tsakanin 'yan takarkaru daban-daban da sukan fito domin neman darewa kan mukamai daban-daban.

Babban abin dadi a irin wannan tsari, shi ne na yadda yawa ko kuma adadi kan yi tasiri wajen hukunci maimakon mutum daya ko biyu su zauna su yanke hukunci kan abin da ya shafi jama'a baki daya.

Wa ya cancanci yin zabe?

A tsarin dokar zaben Najeriya da kuma tsarin mulkin kasar, duk wanda ya kai shekaru 18 da haihuwa, to ya cancanci kada kuri'a a zabukan kasar.

Sai dai baya ga kaiwa shekaru 18, mutum na bukatar ya kasance mai cikakken hankali, sannan kuma ya samu katin rajista na hukumar zabe kafin ya kada kuri'a a lokacin zabe.

Hakazalika, dokar zaben Najeriya ta 2010, ba ta baiwa 'yan kasar da ke zaune a kasashen waje damar kada kuri'a a zabukan kasar ba, idan ba sun dawo Najeriyar ba ne a lokutan zaben.

Domin bayyana ra'ayinku da kuma abubuwan da ke faruwa a yankunanku a lokutan zaben, sai ku aiko mana da bayanan ta dandalinmu na Latsa BBC Hausa facebook ko ta Latsa Twitter, ko kuma ta e-mail a Latsa hausa@bbc.co.uk ko kuma ta gurbin da ke kasa.

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.