Kotu ta hana INEC yin zabe a wasu jihohi

Jega
Image caption Hukumar zaben dai na cikin tsaka mai wuya

Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta ce Hukumar Zaben kasar INEC ba ta da ikon gudanar da zabukan Gwamna a Sokoto da Adamawa da Kogi da Bayelsa da Cross Rivers sai 2012.

Kotun ta ce wajibi ne a kyle gwamnonin su kammala wa'adinsu na shekaru hur-hudu, kamar yadda tsarin mulkin kasa ya tanadar.

Hukumar zaben dai ta bayyana aniyarta ta gudanar da zabukan Gwamnoni a jihohin biyar ne bisa la'akari da wani tanadi a dokar zabe ta kasar.

Wasu kotunan sauraren karrakin zabe sun soke zabukan Gwamnonin biyar ne bayan zaben su a shekara ta dubu 2007.

Bayyana hukunci

Alkalin kotun mai shari'a Adamu Bello, ya kafa hujja da hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke a baya na cewa wa'adin gwamnan jihar Anambra Peter Obi ba zai kare ba, sai ya kammala shekaru hudu daga ranar da yayi rantsuwar kama aiki.

Babban lauya Lateef Fabemi wanda ya jagoranci tawagar lauyoyin da suka wakilci gwamnonin, kuma ya bayyana cewa:

"Hukuncin ya kawar da wani babban lamari wanda ka iya kawo cikas ko rudani a kasar nan. A yanzu ta fito fili cewa babu zabe a wadannan jihohi a watan Afrilu".

Shi ma lauyan INEC Hassan Liman ya ce za su gabatar da hukuncin kotun ga Hukumar, domin daukar matakin da ya dace.

Wasu masu sharhi na ganin hukuncin ka iya zamowa koma baya ga hukumar zaben kasar, wacce a yanzu haka ke fama da dimbin kararraki a gaban kotuna kan zabukan da take shiryawa na watan Afrilu.