Ana raba sakonnin neman fita zanga zanga a Kamaru

Ministan sadarwar kasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya kira wani taron manema labaru domin ya amsa wasu tambayoyin da suka shafi yadda al'amurra suke tafiya a kasar.

Wannan dai ya biyo bayan wata aniyar da wasu yan kasar suke da ita ta kiran wata zanga zangar nuna kin jinin Gwamnati a gobe a birnin Douala.

Sai dai Ministan ya ki ya danganta wannan taro manema labarai da waccan aniya da wasu ke da ita.

To amma duk da haka akasarin tambayoyin manema labarun sun kasance ne a kan yanayin siyasar da kasar ke ciki a halin yanzu ne.

Wata Kungiyar Yan Kamaru mazauna kasashen waje dai ta kira da a gudanar da zanga zangar neman kawo karshen mulkin Shugaba Paul Biya a kasar ta Kamaru .

Ana ta rarraba kasidu tare kuma da aikewa da sakunni ta hanyoyin sadarwa na internet na neman jama'a su fita su yi zanga zangar.