Wani dan Najeriya yayi kashin daurin hodar ibilis 65

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya - NDLEA -ta ce babu sauran mafita ga masu fataucin miyagun kwayoyi ta kofofin shiga kasar.

Hukumar ta bayyana hakan ne jim kadan bayan kama wani mutum da ya yi kashin kullin hodar Ibilis guda 65 a daren jiya.

Mutumin mai suna Dunu Chukwunyere Enoch an cafke shi ne ranar 16 ga watan Fabrairu na bana ,kuma tun lokacin ake sa ido kansa.

Shi ne dai Dan Najeriya na 7 da hukumar ta kama tun makon da ya wuce dangane da laifukan da suka jibanci tu'ammali da miyagun kwayoyi.

Najeriya dai ta fara samun hanyar samun nasarar yaki da fataucin miyagun kwayoyin ne bayan tashi tsayen da ta yi, da kuma samun taimakon bayanai da kayan aiki daga waje.