Kotu ta ce babu zabe a jihohi biyar a Nijeriya

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Farfesa Attahiru Jega

Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta yanke hukuncin cewa hukumar zaben kasar wato INEC ba ta da ikon gudanar da zabukan gwamna a wasu jihohi biyar na kasar, a zaben kasa baki daya da za a yi a, watan Afrilu mai zuwa.

Kotun ta ce wajibi ne a kyale gwamnonin da suka hada da na Sakkwato da Adamawa da Kogi da Bayelsa da kuma Cross Rivers, su kammala wa'adinsu na shekaru hur-hudu, kamar yadda tsarin mulkin kasa ya tanadar.

Hukumar zaben dai ta bayyana aniyarta ta gudanar da zabukan Gwamnoni a jihohin biyar ne bisa la'akari da wani tanadi a dokar zabe ta kasar.

Wasu kotunan sauraren karrakin zabe sun soke zabukan gwamnoni biyar ne bayan zaben su a shekara ta 2007.