'Wayar salula na illa ga kwakwalwa'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Matasa sun fi amfani da wayar salula

Wani bincike da cibiyar lafiyar ta Amurka ta gudanar ta gano cewa wayoyin salula na da illa ga kwakwalwar bil'adama.

An dai gano cewa ana samun karin yawan sukari a kwakwalwa bayan minti hamsin da gama amfani da wayar salula.

Binciken wanda aka wallafa a wata kasidar kungiyar likitocin Amurka ta ce ba'a tantance iya illar da wayar ke yi ba.

Amma wasu masana a Burtaniya sun musanta binciken a yayinda su ka ce, babu kanshi gaskiya game da batun, saboda a cewar su wayar salula bata barazana ga rayuwar al'umma.

Yawaitar amfani da salula

A 'yan shekarun nan da aka samu karuwar amfani da wayar salula, ba'a samu rahoto game da illar amfani da wayar ba ga dan adam.

Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)

Wani binciken da aka dauka a kan masu amfani da masu wayar wajen 420,000 a kasar Denmark, bai nuna ko amfani da wayar salulu na haddasa ciwon daji ba.

Amma wani gwaji da aka gudanar akan mutane 47, an lurra cewa akwai wani sinadari da ba'a gani da ido da wayar ke amayar da shi.

Wannan sinadari dai na illa ga kwakwalwa, amma ba'a gano takamaimai abun da illar zai haddasa ba.

Gwaji

A gwajin da aka gudanar an sanya wayoyin salula biyu an kunnuwa biyu na kowani mutum. An kashe waya guda a cikin daya kuma aka kashe muryar, saboda kada wanda ake gwajin a kansa ya san wanne ne a cikinsu ke kunne.

An dai gwada kwakwalwansu inda aka gano cewa akwai karin sinadarin glucose da kashi bakwai a bangaren kunnen da ke kusa da wayar da take kunne.

Binciken dai ya yi la'akari da yadda wayar salula ka shafar yadda kwakwalwa ke aiki.

"Har ila yau sakamakon binciken bai nuna mahimmacin wannan abu ko kuma akasin haka ba."

Farfesa Patrick Haggard, wani masani a harkar kwakwalwa da ke jami'ar kimiyar kwakwalwa da ke Landon ya ce; "Binciken na da mahimmacin domin a yanzu haka mun sa cewa wayar salula na iya illa ga kwakwalwa."

"Mun dai lurra cewa illar na rage zurfin tunani."

"Har wa yau, idan mun kara bincike mun ga cewa wayar salula ba ta da wata mumunar illar ga kwakwalwa, dolene mu kara wani bincike muga ko tana da illa ga rayuwar dan adam".

Farfesa Malcolm Sperrin, Direkta a asibitin Royal Berkshire cewa ya yi; "Binciken na da matukar mahimmacin musamman yadda ya nuna inda wayar ke sanya karuwar wasu sinadarai a kwakwalwa."

"Dolene mu kara aikin wajen gudanarda binciken da zai duba alakar illar da wayar ta ke ma kwakwalwa da kuma lafiyar jama'a."

"Kuma na yi matukar farin cikin yadda aka gudanar da wannan bincike ba tare da rayuwar wasu ya shiga cikin wani hatsari ba".