Peru ta dakatar da hulda da Libya

shugaban kasar Peru Alan Garcia

Gwamnatin kasar Peru ta dakatar da duk wata huldar diplomasiyya da kasar Libya saboda bude wa farar hula wuta da jami'an tsaron kasar ke yi.

Peru din dai ta zama kasa ta farko da ta dauki irin wannan mataki tun daga lokacin da aka soma zanga-zangar nuna `kin jinin gwamnatin Libya.

Ministan hulda da kasashen waje na Peru, Jose Antonio Garcia Belaunde ya ce, yana fatan sauran kasashen yankin Latin Amurka ma za su dauki irin wannan mataki.

Sai dai kuma kawayen Libyan a yankin na Latin Amurka da suka hada da Cuba da kuma Venezuela sun yi kira ga abin da suka ce, kasashe masu son yin mamaya su daina tsoma baki a sha'anin kasar Libya.