Masu adawa a Libya sun bazama kan tituna

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dubban masu adawa da gwamnatin Libya a yankin gabashin kasar

Dubban masu adawa da gwamnatin Libya a yankin gabashin kasar sun ci gaba da murnar abinda suka kira, samun 'yan cin kansu, yayin da shugaban kasar, Kanar Mu'ammar Gaddafi yake kokarin samun iko da yankin yammacin kasar.

Masu zanga-zanga a biranen Benghazi da kuma Tobruk sun bazama kan tituna suna shewa.

Wata mace soja mai suna, Salma Faraag Issa a garin Tobruk tace su mata ne soja dake gadin garin cikin dare, kuma duk da basu da makamai basa tsoron komai.

Tuni dai rundunonin soja da dama dake gabashin Libya suka bayyana cewa sun hade wuri guda da masu yiwa gwamnati bore.