An zartar da dokar samun bayanai a Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Ana sa ran hakan zai karfafa dimokuradiya

A Najeriya, majalisar wakilai ta kasar ta amince da kudurin dokar ‘yancin neman bayanan ayyukan gwamnati da aka jima ana cece – ku-ce a kanta.

Dokar dai za ta bayar da ‘yanci ne ga neman bayanai daga hukumomin gwamnati.

Idan aka amince da ita, ana sa ran ta taimaka ga tsarkake al'amura a harkar gwamnatin Najeriya, ta hanyar kawar da kumbiya-kunbiya da sarkakkiyar aikin gwamnati wajen tafiyar da ayyukan gwamnatin.

‘Yan jarida da kungiyoyin kare hakkin bil adama suna cikin wadanda suka fi marhabin da wannan doka.