Gaddafi ya kara yin jawabi ga jama'ar Libya

Muammar Gaddafi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Muammar Gaddafi

Shugaban Libya, Muammar Gaddafi ya yi jawabi ga jama'ar kasar sa a daidai lokacin da ake fuskantar tarzomar da ta kai ga wani bangaren kasar kubucewa daga hannunsa.

Kanar Gaddafi ya dora alhakin tashin hankalin da aka fuskanta akan Osama Ben Laden, Jagoran kungiyar Al-Qaeda, yana mai cewar abun da ya faru ta'addanci ne na kasa da kasa.

Haka nan kuma ya zargi wasu mutanenda ba'a san ko su wanene ba da bayar da kwayoyi ga yara yan kasar Libya.

Shugaba Gaddafi ya kuma yi kira ga iyaye da su kwabi 'ya 'yansu sannan su tabbatar sun koma gidajensu.