Mutane ashirin sun mutu a Somalia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption mayaka a kasar Somalia

Akalla mutane ashirin ne suka mutu sakamakon fada mafi muni cikin 'yan watannin nan a Mogadishu, babban birnin Somalia.

Dakarun gwamnatin kasar da kuma na kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika, wato AU ne suka kai hari a wuraren da kungiyar Al-Shabab ke rike da iko.

Wani kakakin gwamnati ya ce, sun kwace iko da wasu daga cikin muhimman wuraren da 'yan tawaye suka kame, da suka hada da ginin ma'aikatar tsaro.

Hakazalika, an bada rahoton cewa, mayakan kungiyar Al-Shabab sun nuna gawarwakin dakarun kiyaye zaman lafiya na AU biyar.