Taron wanzar da zaman lafiya a Najeriya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

A Najeriya, yayin da ake tunkarar zaben kasar, wasu kungiyoyi masu zaman kansu ,na cikin gida da kasashen waje na ci gaba da kokarin jan hankulan jama'a, gwamnatoci, da 'yan siyasa game da muhimmancin wanzar da zaman lafiya a tsakanin al'umma, ta hanyar shawo kan matsalolin da ke haddasa tashe-tashen hankula.

Kungiyar Tarayyar Matasa Masu Fafitikar Zaman Lafiya a kasashen Duniya ta bude babban taron Jakadun Wanzar da Zaman Lafiya na kwanaki biyu a Maiduguri domin tattaunawa akan yadda za'a shawo kan matsalolin da suka shafi tsaro da tunkarar zaben watan Aprilun wannan shekarar.

Jihar Borno dai na daga cikin jihohin Najeriyar da yanzu haka ke fuskantar matsalolin da suka shafi tsaro, lamarin da ke jefa jama'a cikin zullumi.

Wasu mahalarta taron sun danganta matsalar talauci a matsayin wasu daga cikin dalilan dake haddasa abkuwar tashe-tashen hankula a kasar.