Gaddafi zai rabawa al'ummar Libya kudi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kanal Gaddafi

Shugaban kasar Libya Kanal Gaddafi ya bada umarnin rabawa al'ummar kasar kudi.

Gaddafi ya ce kowani iyali za su samu dalan Amurka dari takwas, domin ya taimaka musu a yayinda ake samu karin farashin kayayakin abinci.

Shugaban kasar, har wa yau ya ce ya bada umarnin karin albashin ma'aikata da kashi dari da hamsin.

Shugaba Gaddafi ya yi wannan alkawarin kwana guda bayan da yayi jawabi ga al'ummar kasar, inda ya zargi Osama da tunzura matasan kasar domin su yi bore.

Rahotanni sun ce ana ci gaba da jin karar bingidogi a Al-Haddaykh yayin da kuma a gabashin kasar wasu shugabannin kabilu tare da 'yan siyasa suka gudanar da wani taro a yunkurin da suke yi na hada kai don tunkarar dakarun shugaba Gaddafi.

Yanzu haka dai kasashe duniya na ci gaba da aikewa da jiragen sama da jiragen ruwa don kwashe 'yan kasashen su daga Libya, inda kasar Turkiya ta ce ta kwashe fiye da 'yan kasar ta su dubu bakwai ta jiragen ruwa.