Zanga-zanga a babban birnin Iraqi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga a Iraqi

Daruruwan mutane ne su ka hallara a dandali mafi girma a birnin Bagadaza da ke Iraqi, domin gudanar da zanga-zanga kan halin da al'ummar kasar ke ciki.

Masu zanga-zangar dai na korafi ne kan rashin ayukan yi da yadda cin rashawa ke kara yawa da kuma rashin abubuwan more rayuwa a kasar.

Masu zanga-zangar sun hau kan mayan tituna da anguwanni domin nuna rashin jin dadin su.

Yayinda a wasu kasashen labarawa masu zanga-zanga ke neman a sauya gwamnatocin su, na Iraqi na neman gwamnati ne ta inganta rayuwarsu.