Jam'iyyar CPC zata daukaka kara

Image caption Jam'iyar adawa ta CPC a Najeriya

A Najeriya,kwamitin amintattu na jam'iyyar CPC ya ce zai daukaka kara akan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi inda ta tabbatar da Senata Garba Yakubu Lado Danmarke a matsayin wanda ya lashe zaben fid-da-gwani na takarar mukamin Gwamna a karkashin jam'iyyar CPC a jihar Katsina.

Kwamitin ya yanke shawarar ce bayan daya wani taron gaggawa da ya gudanar a daren jiya a Abuja babban birnin kasar.

Shi dai Senata Lado Dan marke ya shigar da kara ne gaban kotun, inda ya kalubalanci matakin da jam'iyyar CPC ta dauka na gabatar da Honorabul Aminu Bello Masari a matsayin dan takararta ga hukumar zaben kasar.

Jam'iyar CPC dai na fama da rikice rikicen cikin gida a wasu jihohin kasar sakamakon zabubbukan fidda gwani na 'yan takarar mukamai a karkashin jam'iyar a zaben kasar dake tafe.