Gwamnatin Libya zata ba da toshiyar baki

Masu zanga zanga a Libya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An gudanar da zanga zanga a birnin Tripoli

Kwana daya bayan jawabin da shugaba Moummar Gaddafi yai a gidan talibjin din kasar, inda yai Allah wadai da masu yi masa bore , yanzu gidan talibijin din ya ce gwamnatin kasar ta ce zata bada kudi mai yawa ga jama'ar kasar a matsayin tallafi.

Gwamnatin ta ce zata bada kudi da yawansu ya kai dala dari takwas ga dukkanin iyalan kasar a cikin watanni biyu domin a taimaka masu wurin shawo kan matsalar tsaddar abincin da ake fama da ita a kasar.

Har ila yau gwamnatin tace za'a karawa ma'aikata gwamnata albashi da kashi dari da hamsin cikin dari, ya yin da aka kuma ninka albashi mafi kankanci.

A wani labarin kuma dazu a birnin Tripoli dakarun dake goyan bayan Kanal Gaddafi sun wuta kan masu zanga zanga.