Kungiyar NATO za ta yi taro kan Libya

Jakadun kungiyar tsaro ta NATO zasu yi wani taron gaggawa yau a Brussels akan halin da ake ciki a kasar Libya.

Sakatare Janar na kungiyar NATO, Anders Fogh Rasmussen, ya ce ya kira wannan taro ne domin tuntubar juna akan abun da ya kira yanayin da ya ke sauyawa cikin gaggawa a kasar ta Libya.

Hakazalika a birnin Geneva , hukumar kare hakkin biladama ta MDD, ta fara wani taron gaggawa inda ake ganin zata bukaci a kori kasar libya , matakin da ba'a taba dauka ba kan wata kasa wadda memba ce a majalisar.

A halin da ake ciki, Shugaban Amurka, Barrack Obama, yayi magana ta wayar tarho tare da Shugabannin kasashen Birttania da Italia akan wanann rikici.

Faransa da Burtaniya sun yi kira ga kwamitin sulhu na MDD akan ya sanyawa Libya takunkumi kuma a hana sayar mata da makamai