Shirin kwashe 'yan Najeriya daga Libya

Gwamnatin Najeriya tace tana ci gaba da kokarin ganin yadda zata kwaso duk yan kasarta dake Libya wadanda ke san komawa gida, yayin da ake ci gaba da rikicin neman shugaba Gaddafi ya sauka daga kan mulki.

Yanzu haka gwamnatin Najeriyar ta ce sama da mutane dari biyar ne suka nuna bukatarsu ta barin kasar ta Libya.

Tuni kasashe da dama suka fara kwashe mutanansu dake Libya, yayin da wasu kuma suka nemi hanyar kaiwa da kafarsu.

Rahotanni sun ce mutane da dama da suka tserewa rikicin kasar Libayan sun nufi jamhuriyar Nijar dake makwabtaka da ita