Wani ya cinnawa kansa wuta a Senegal

Image caption Shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade

Rahotanni daga kasar Senegal na cewa, wani mutum ya cinnawa kansa wuta jiya Juma'a a kusa da fadar shugaban kasar.

Kuma hakan ta abku ne 'yan kwanaki bayan wani tsohon soja da ya rasa aiki ya mutu sakamakon kokarin kashe kansa da yayi ta wannan hanya.

Ma'aikatan kiwon lafiya sun shaidawa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa, mutumin dan shekaru talatin da uku, wanda yake aiki a wani shago yana ci gaba da jinya asibiti.

Mahaifin mutumin dai ya fadawa kafofin yada labarun kasar cewar, dansa ba shi da alaka da duk wata harkar siyasa.