Zanga-zanga a titunan kasashen larabawa

Masu zanga zanga a kasar Masar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An gudanar da manyan zanga-zanga akan titunan kasashen larabawa

An gudanar da manyan zanga-zanga akan titunan kasashen larabawa.

A kasar Iraqi inda zanga-zangar ta fi maida hankali ga yaki da cin hanci da rashawa da kuma matsalolin tattalin arziki, an kashe akalla mutane goma sha daya a karawar da aka yi da jami'an tsaro.

A kasar Tunisia ma dai dubban mutane ne suka yi zanga-zangar neman maye gurbin gwamnatin rikon kwaryar kasar da ta maye gurbin gwamnatin Zaine Al- Abidin Ben Ali.

A birnin Alkahira ma mutane sun hallara a dandalin Tahrir suna kiran a kawar da duk ministocin dake da nasaba da tsohon shugaba Hosni Mubarak.